KEƁAƁƁUN KALMOMI A TATSUNIYAR HAUSA
Main Article Content
Abstract
Aro da ƙirƙira wata ɗabi’ace wacce ta zama ruwan dare game-duniya, musamman ga duk wani harshe mai son ya ga ya ci gaba. Sannan kuma harshe yana aro ya mayar da abin da ya ara ya zama na sa, wannan ya sa harshen Hausa ya zama kamar hankaka mai da ɗan wani naka, sau da dama wasu kalmomin da harshen Hausa ya aro ba a iya fahimtar aro ne aka yi. Haka ita kuma tatsuniya wadda Hausawa suke amfani da ita wajen saita tunanin al’umma, sannan kuma da yadda mawari ke amfani da wasu kalmomi, waɗanda suka keɓanta da taurarin cikin tatsuniya, waɗanda ana iya fahimtar su ne kawai ta hanyar nazari da kuma bincike. Saboda haka wannan muƙala ta fito da wasu keɓaɓɓun kalmomin da ake iya fahimta a cikin tatsuniya, waɗannan kalmomi suna taimaka wa harshe ya ci gaba da bunƙasa, sannan kuma a ƙara samun sababbin kalmomin nazari a hanyar ilmi, waɗanda masu nazari za su faɗaɗa nazari da kuma masana su amfana wajen bunƙasa ilmi, domin keɓaɓɓun kalmomi suna ƙara harshe ya matsa daga inda yake zuwa wani bagire na ci gaban wannan al’umma dangane da hulɗar su da harshensu a al’amuransu na yau da kullum.
Article Details
This work is licensed under a Creative Commons Attribution-NonCommercial-NoDerivatives 4.0 International License.