GUDUMMUWAR FINA-FINAN ‘INDIYAN HAUSA’ WAJEN BUNQASA RUMBUN KALMOMIN HAUSA
Main Article Content
Abstract
Babbar buqatar mai aikin fassara shi ne ya iya juyar da wani saqo na wani matani da aka samar daga wani harshe zuwa harshen da yake fassarar a cikinsa. A qoqarin aikin nasa kuwa yana da dama ya yi amfani da hikimomi da dabaru mabambanta domin ganin ya cim ma manufa. Wannan muqala mai suna ‘Gudummuwar fina-finan ‘Indiyan Hausa’ wajen bunqasa rumbun kalmomin Hausa’, ta yi nazari ne ga irin kalmomin da masu fassara fina- finai daga harshen Indiyanci zuwa Hausa suke qirqira su kuma yi amfani da su a wajen aikin fassarar tasu. Maqalar ta yi qoqarin kawo ire-iren waxannan qirqirarrun kalmomi ne da kuma ma’anarsu. Haka kuma ta kawo wasu kalmomin da tun asalinsu na Hausa ne amma kuma sun samu qarin wata ma’ana daga wurin masu aikin fassarar, inda su ma aka kawo su da ma’anar da aka san su da ita ta ainihi, sannan kuma aka kawo sabuwar ma’anar da aka liqa musu. A qarshe maqalar ta tabbatar da cewa masu aikin fassara fina-finan ‘Indiyan Hausa’ suna ba da gummuwa wajen bunqasa harshen Hausa ta hanyar samar masa da sababbin kalmomi.
Article Details
This work is licensed under a Creative Commons Attribution-NonCommercial-NoDerivatives 4.0 International License.